Wednesday, November 28, 2007

Tskanin Yar'adua da Buhari

Bismillahir Rahmanir Rahim
Tun daga sanda akayi zabe a cikin watan Aprilu na bana, wanda yakare da rantsarda Umar Musa Yar'adua, a matsayin zababben shugaban Najeriya, ra'ayoyin mutane suka kasu biyu, da masu goyon baya da masu neman a soke wannan zabe wanda daga karshe kuma shi dan takara da yasha kaye kamar yadda akace wato Janar Muhammad Bukhari me ritaya da jam'iyyarsa suka shigar da kara a gaban kotu suna kalubalantar wannan zabe, da yin kira ga kotu da ta rushe wannan zabe, kamar yanda da dama daga cikin kungiyoyi na gida dana waje sukayi. Yanzu dai ga lokaci na tafiya kuma ga bisa dukkan alama, sashin shari'ah yasamu gyaruwa a wannan lokacin ta inda yasami nasaran soke wasu daga cikin zabubbukan da'akayi na wasu gwamnoni, da wasu yan majalisu na jahohi ko na tarayya, wanda wannan abune da za'ayi tamaka . Asashi daya kuma Umaru Musa Yar'adua gyara yake tayi na abubuwan da gwamnatin da tagabata tayi, wanda bana kan ka'ida ba, kama daga sayarda matatar mai wato NNPC da makamantansu, dayin kokarin samar da man petur a kasa, duk da wasu suna ganin abinda yakeyi kamar siyasa ce kawai saboda cewa beci zabe ba, wanda wasu kuma sun dauka cewa zezo ne yazama dan amshin shatan Obasanjo, to amma koma me kenan dai abubuwa dayakeyi na gyara yakamata ayaba masa akansu, dukda dama hakki ne na kowani shugba daya aikatasu, kai fiyema. Sannan kuma Sarakuna da dattawan Arewa, sukayi taro suna babatu da cewa " Janar da Atiku yakamata su janye wannan karatasu" da dalilin cewa ai duk kansu yan Arewa ne kuma musulmai, na'am wannan magana tasu haka take amma sedai abin tambaya shine meyasa su wannan dattawa kamar yadda ake kiransu aikata wannan aiki, kuma maganar da shi Janar yayi ta bani sha'awa cewa, ai ba Yan Arewa kadai suka zabeshi ba Yan Najeriya ne gaba daya, kuma baso ake a tabbatar da adalci ba kuma shari'a ai abinda zatayi kenan, to mezesa baza'a ajiraba aga abindan kotu zata zartar. kuma kalmar da Yar'adua yayi na cewa duk abinda kotu ta zartar shi zeyi biyayya akan haka kuma bedamu ba, hakan yana nuna cewa yanada halin dattijontaka, kuma abinda yakamacemu mu yan najeriya, da Yan Arewa masu kishi daga cikinsu ba wadanda suka kasheta ba, da mutemaka ma gaskiya da kokarin binta, kuma mutuna cewa kakannin mu ba wani abu yasa har yanzu ake ganin girmansu ba face gaskiya da sukayi da riko da Addininsu irinsu SARDAUNA dasu TAFAWA BALEWA, kuma mudunga karanta tarihi na magabatanmu domin ko ba komi ai Tarihi maimaita kansa yakeyi kuma duk matansa da basu san tarihin magabatansu ba to babu tayanda zasuyi su cigaba. Allah muke roko daya bamu shuwagabanni masu tsoron ALLAH, dazasu kawo cigaban kasa da Addininmu Amiiiiiiiin.

No comments: