Friday, January 18, 2008

KUNTATAWA FALASDINAWA AMFANIN WANENE?

KUNTATAWA FALASDINAWA AMFANIN WANENE?

Wahal-halu da Kungiyar Hamas take fuskanta da Kunci da take ciki, tun sanda ta sami nasaran lashe zabe wanda ya rikitar da shugaba Mahmoud Abbas da Kungiyarsa ta Fatah inda ta kasa zama zab’I na farko ga Mutanen Falasdin duk da irin iko dashi me girma a cikin gida da kuma waje, kai da temako ma sananne daga wajen Yahudawa masu mamaya, hakan yasasu k’in koda temakekeniya da Hamas, saboda K’okarin karya ta bayan tasami daman kafa hukuma, se Kuntata daga wajen (tsohuwar Kungiya) wanda har yanzu bata gushe ba tana zaune cikin rud’u cewa itace jagora a al’amarin.

Daga cikin wadanda suka bada gudunmawa wajen yin batanci ga Hamas har da Sannannun tsofaffin nan da Ihunsu yafi aikinsu yawa a kafafen watsa labarai na gida da na waje, musamman bayan abinda yafaru na gyara a goma sha hudu ga watan Yuni a Shekaran data shud’e, da tsoratarwa gameda Hamas, da sunan wai a rayawarsu tayi juyin Mulki ga hukauma, da nufin kafa kasa ta musulunci, kuma shin wacece hukuman in ba Hamasa ba?

hakika Mutanen Falasdinu sun d’and’ani daci guda biyu Na: Matakin rashin girmama dan Adam da Hukumar Mahmoud Abbas takeyi masu, da kuma: takurasu akan su kaurace ma Kungiyar Hamas, da kuma jefa shakka gameda Manufofinta, kai dama Manufofin wadanda suke cikinta, Saboda hakane sukayi aiki wajen baza duk kan k’okarinsu wajen sanya Isra’ila ta mamaye zirin Gazza, da karya Kungiyar, domin su koma kan iko bayan binkito Asirin me yawa da suke boye a wajensu na abin Kunya da sukayi, wanda aka bayyanar da cewa sun kasance suna tafiya akansu domin cimma burikansu na ciwo. Kuma daga cikin abin takaici shine hukuman tabada umarnin rufe Kungiyoyin agaji guda dari da uku (103) wadanda suke aikin jink’ai a Zirin Gazza da gabar Yamma da kogin Jordan, ta tuhuman wai sun sabama tsari! To me yasa ba’a gano hakaba se bayan rushewan sashin tsaronsu? Gaskiya itace Hukuman Falasdinawa karkashin Jagorancin Mahmoud Abbas da Manya Manayan magunansu masu k’iba suna zartar da ajandoji ne na Kasar Amurka da Isra’ila a cikin yakinsu ga ayyukan alkhairi wanda hakan abune dayake bayyane wajen kowa.

Wannan bari d’aya kenan, a gefe daya kuma zamuga wadanda ake ambata sun kunyata kawunansu, da kiraye – kirayen dasukewa mutanensu cewa su sake lale gameda hukumarsu da aka dakatar wato Kungiyar Hamas, wannan ke nuna kwadayinsu na Nufin sayan mutane day’an kudi marasa yawa alhali kuwa Falasdinawa sunfi karfin a yaudaresu, Sannan me yasa suka lalata wutan lantarki wanda suna daga cikin kayan more rayuwa na asali? Me yasa suka hana wasu kayan hukuma aiki, misali takardar tafiya wato Passport da yin sheda akan takardu da sauransu wanda rayuwa bata yiwuwa face dasu kuma shin akwai maslaha a yin hakan?

Tabbas wannan Kungiya ta marasa kishi, Bawai tana munana ma Hamasa bane kawai, A’a Falasdinawa take munanawa masu hakuri, wadanda suka wayi gari a yau basu da wata k’ima a wajen K’ungiyar Fatah me mulki dake jagoranci a Gabar yamma da kogin Jordan, kuma Falasdinawa sunfi karfin a rabasu da dabi’unsu da Manufofinsu. Hakika wasu daga kafafan watsa labarai na duniya sunyi nuni da cewa Kumgiyar Hamas zata kara K’arfi, wannan shine dalilin dayasa hukumar, tak’i ta dena aiwatar da dokokin korar ma’aikata, da jami’an tsaro da sauransu saboda zalunci da kuma kasancewarsu yan K’ungiyar Hamas ne.

Gasunan a yau suna ingiza wawaye a zirin Gazza wajen tada fitina da haifar da matsaloli, amma Mutanen Falasdinu masu hakuri abinda yasamesu na kunci ya ishesu. Kuma Mummunan Makirci baya komawa se ga masu aikata shi.

Thursday, January 10, 2008

Gamji Dan K'warai

Gamji Dan Kwarai, Allah yayi masa Rahama Amin. A 15-01-2008 yake cika shekaru 42 da kwanta dama, kuma har yanzu yana nan a zukatan Y'an Nijeriya, ba'a manta dashi ba, Anamasa Addu'a, Allah yajikan mazan K'warai. To wai Meyasa wanda suke raye ba'a ambatansu? se matattu kuma tun ayyukan dasukayi wa kasa duk tsawon wannan shekarun, har yanzu ana amfana dasu, irinsu Jami'ar Ahmadu Bello da sauransu, ina shugabannin mu wanda su Sardauna suka rena? Ina Yan k'asa na kwarai? shin kuna tsammanin a bayan ranku za'a tuna daku? Yakamata ku sake tunani kusan irin abinda zaku aikatawa Al'ummarku tun kafin Ajali yazo maku ayimaku Addu'a ba'a la'aceku ba, Sarakuna ku dauki tafarki da Sardauna yabi domin Martabar ku ta dawo a Idanun jama'a, ba wai kutaru a gidan Sardauna, ba kuyi jawabai shike nan, a watse A'a kuyi abinda ze daukaka Al'ummar mu, dare beyiba ga duk wanda yake darai kowa yayi da kyau zega da kyau Allah ya jikansu Ahmadu Bello Amin.